Labarin dake shigo mana daga Damaturu babban birnin Jihar Yobe na bayyana cewar Gwamnonin jihohi shida da suka ha?a yankin arewa maso gabas sun gudanar da ganawar sirri karo na shida a Damaturu, babban birnin jihar.
Taron ya samu jagorancin shugaban gwamnonin kuma gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum yayin da gwamna Mala Buni na Yobe ya karbi bakuncin shi.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamna Zulum ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook a ranar Litinin.
Gwamna Mala Buni na Yobe da gwamna Inuwa Yahaya na Gombe sun samu halartan taron yayin da gwamnonin jihohin Taraba, Adamawa da Bauchi suka tura wakilcin mataimakansu.
Da yake jawabin bude taron a gidan gwamnatin Yobe, Zulum ya yi bayani kan ayyukan kungiyarsu, da kuma ?ara jaddada kudurin ?ungiyar na tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Shugaban gwamnonin yace cigaba da aka samu a yaki da ta’addanci kwanan nan wata alama ce ta kawo karshen matsalar tsaro a arewa maso gabas. Ya kuma yi kira ga jami’an tsaron soji su ?ara zage dantse wajen share ta’addanci da yan ta’adda a yankin baki ?aya.
“Ina kira ga sojojin Najeriya su dumfari ma?oyar yan ta’adda wa?an ba su shirya aje makaman su ba, ya zama wajibi mu bi ta kansu mu gama dasu.
“Idan har muna son kawo karshen wannan rikicin sai mun tabbatar da an bi har ma?oyar yan ta’addan nan an aika su lahira.” Zulum ya ?ara da cewa har sai an kawo karshen Boko Haram sannan za’a fara ganin cigaba a dukkan jihohi shida.
A jawabinsa na maraba, gwamna Mala Buni ya ?ara jaddada shirinsa na sadaukarwa ga kudirorin ?ungiya. Buni ya yi tsokaci kan yanayin tsaro, da nasarorin da sojoji ke samu, da kuma bukatar masu ruwa da tsaki su cigaba da ha?a karfi wajen ya?i da yan ta’adda.
