Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta garga?i ?an ?asa ciki har da sarakunan gargajiya da ?an siyasa da malaman addinai da cewa su guji yin duk wani abu da zai jawo sa?a doka da oda.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata mai ?auke da sa hannun mai magana da yawunta PN Afunanya, DSS ta ce ta yi wannan garga?i ne don fahimtar da ta yi na yadda wasu mutane ke neman mulki ido a rufe da suke amfani da hanyoyin da ba su dace ba ta wajen tunzura ?an ?asa da kuma ruruta wutar siyasa.
Wannan sanarwa ta DSS ta zo ne a daidai lokacin da yanayin rashin tsaro ke ?ara ta’azzara musamman a yankin arewa, inda mutane da dama ke nuna fushinsu kan abin da suke kira gazawar gwamnati wajen kasa magance matsalar.
Sanarwar ta ce: “Tuni masu irin wannan a?ida sun fara siyasantar da batun rashin tsaro a wasu sassan ?asar bisa wasu dalilai na son kansu.
“Da yawansu suna amfani da damar yanayin da ake ciki don jawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ?an ?asa, da neman suna da ko kuma sanya ?asar cikin matsala.”
Ga dai sa?onnin da ke ?unshe a cikin sanarwar kamar haka:
Hukumar ta garga?i dukkan masu hannu cikin irin wa?ancan laifuka da ta ambata da su guji aikata su.
Ta kuma nemi ?an siyasa da su yi komai bisa doka tare da gujewa maganganu ko ayyukan da za su iya kunna wutar rikici gabanin za?ukan shekarar 2023.
“Masu saita tunanin al’umma kamar malamai da sarakunan gargajiya ma ana bu?atar su iya bakinsu su kuma guji kalaman tunzura mutane,” in ji sa?on.
