Rahoton dake shigo mana daga Lafiya fadar gwamnatin jihar Nasarawa na bayyana cewar Gwamnan Jihar Sule Abdullahi yace ko shakka babu ‘yan Najeriya za su yi kewar Shugaban ?asa Buhari idan ya sauka daga mulki a 2023.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labaran gidan gwamnati bayan haduwarsa da shugaban kasa ranar Talata. “Na sanar da shugaban kasa cewa ‘yan kasa ba za su lura da kokarinsa ba har sai ya sauka daga kujerarsa.
Sule ya bayyana cewa basu tattauna da Buhari akan tabarbarewar tsaro ba. Sai dai ya ce sun tattauna akan wasu abubuwan da shi. A cewarsa: “Mun tattauna da shugaban kasa akan amfani da iliminmu wurin bunkasa matatun gas a Afirka ta yamma wanda ake samowa daga Sagamu zuwa Ikeja don sauran ma’aikatu su amfana.
“Ga kasa irin Najeriya da ta ke da albakatun ma’adanai, ba na tunanin idan mutum ya ce zai gina kamfanonin gas ba kankanin abu bane. Amma mutane ba za su gane ba har sai ya sauka daga kujerarsa. “Idan ya sauka, gas din girki ya wadata sannan ababen hawarmu su ka koma amfani da gas, a lokacin ne za a san cewa Buhari ya yi aiki kuma a dinga yi masa fatan alheri.”
Gwamnan ya ce a cikin gidan gwamnatin ya yi wa Buhari godiya akan yadda ya tallafa wurin samar da zaman lafiya a kasar nan. Ya ce shugaban kasa ya yi kokari kwarai wurin dawo da tsaro a cikin yankinsu, kuma sojojin kasa da sama tare da ‘yan sanda su na yin aiki tukuru wurin bayar da tsaro a kananun hukumomi biyu masu iyaka da Abuja, Toto da Karu.
Ya kara da bayyana farin cikinsa akan yadda Nasarawa ta samu tsaro da kwanciyar hankali, inda ya ce yanzu ana noman rogo da doya sosai a kasar nan, don su ne na biyu.
