Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa sanannen Malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Abdallah Usman Godon Kaya ya janye ikirarin da ya yi kan ma’aikatan lafiya na cewa wasunsu na aikata masha’a yayin da suke aikin dare a asibitocin kasar.
Cikin wani jawabi da ya yi da aka gani a wani bidiyo, malamin addinin Musuluncin ya zargi ma’aikatan lafiyan da mu’amular da ba ta dace ba, ciki har da zina da cin zarafin mata.
Tun da farko jaridar intanet ta Sahelian Times ta ruwaito shehin malamin yana zargin ma’aikatan lafiya da aikata zina yayin wani shirin talabijin da aka haska a tashar talabijin ta Africa TV mai zaman kanta.
Sai dai daga baya ta ce baya malamin ya janye kalaman nasa, bayan da ?ungiyar ma’aikatan jinyan ta ce kalaman nasa ?ata wa ?a?anta suna ne, tare da neman ya janye su.
Ga abin da ya shaida wa BBC baya da aka tuntu?e shi kan kalaman nasa.
Ya gaya wa BBC cikin wani sakon murya da ya aika cewa “Ban yi niyyar cutar da kowa ba, kuma ya kamata mutane su zama masu kyautata tunanin alheri.”
Sheikh Gadon Kaya ya shaida wa BBC cewa wasu ma’aikatan lafiya ne suka fara tuntu?arsa kan wannan lamarin da ke ci gaba da jan hankalin jama’a.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
“Wasu ma’aikatan kiwon lafiya biyu, namiji da mace ne suka kira ni, muna karatu ne suka yi min fatawa, inda suka fadi matsalar da suke fuskanta ta ha?a mace da namiji, wani lokacin a cikin aiki na dare.
“Suka koka, kuma na yi bayani a matsayina na almajiri, mai nusantar da mutane akan aikata daidai.”
Ya ce ya yi bayani ne cewa matukar hakan na faruwa ya kamata a gyara: “Ya kamata a tsare mutunci matan nan da iyalanmu da ‘ya’yanmu gaba ?aya.”
Sheikh Gadon Kaya ya ce bayan da kalaman nasa suka tayar da hankalin jama’a, musamman ma’ikatan lafiya, ya zauna da su, inda ya ce “sun warware min dukkan abubuwan da suka shige min duhu kan wannan lamarin.”
Ya ce ma’aikatan lafiyan sun “yi gungu kuma sun ziyarce ni”.
Ya kuma ce sun sanar da shi cewa labarin da ya yada babu ?amshin gaskiya cikinsa, kuma ya ce ya hujjarsa ita ce “wasu ma’aikatanku ne suka kira ni, suka tambaye ni a karatu kuma na bayar da jawabi, inda na ce a gyara”.
“Laifina shi ne na ce idan wannan abin yana faruwa, na ce a gyara.”
Ya ce bayan da suka “yi min bayani, kuma na yi musu bayani, mun fahimci juna. Sai na ce mu su ‘ba ku fahimci maganganun da ake yadawa ne ba’.”
Ya kuma yi karin bayani, inda yace dalilinsa na biyu na furta wadannan kalaman masu tayar da hankali shi ne domin yana cikin masu yin kira ga al’umma da a rungumi karatun kiwon lafiya domin saboda akwai bukatar su cikin al’ummar kasar.
Shehin ya ce bayanan da ma’aikatan lafiya suka yi kan batun, ya ?aru da wasu abubuwan da a baya bai sani ba.
Sai dai ya kare kansa inda ya ce bai ambaci sunan inda matar da ta yi masa tambayar ta fito ba.
“Ban san daga wace jiha tambayar ta fito ba kuma ban ambaci sunan wata jiha ba, ballantana wasu suce da su nake wannan maganar.”
