Mamallaka Gidajen Talabijin Da Rediyo Sun Kaddamar Da Yaki Da Rashin Tsaro


Rahotannin dake shigo daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Kungiyar mamallaka gidajen rediyo da talbijin da ke arewacin Nijeriya sun bayyana matu?ar damuwa dangane da ayyukan ‘yan ta’adda da mahara da sauran abubuwan assha da ke addabar yankin.

Don haka a ?ar?ashin ?ungiyar Mamallaka Gidajen Rediyo da Talbijin ta Arewa (Northern Broadcast Media Owners Association, NBMOA) sun bayyana cewa za su fara wani aikin fa?akarwa ta hanyar kafafen su a kan wasu daga cikin munanan ayyukan da ke fuskantar Arewa da ma ?asar baki ?aya.

Ita dai NBMOA, ?ungiya ce ta mamallaka gidajen rediyo da talbijin da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ya?a labarai a Arewa wadda aka kafa domin samun cigaban yankin da ?asa baki ?aya tare da tabbatar da ?warewa da bun?asa a harkar aikin rediyo da talbijin a Nijeriya.

A lokacin da ya ke jawabi ga wani taron manema labarai da aka yi a Abuja a ranar Laraba, mu?addashin shugaban ?ungiyar, Abdullahi Yelwa, ya ce ma’aikatan ya?a labarai sun samu kan su a cikin mawuyacin hali dangane da rashin tsaro a Arewa.

Ya nuna cewa an cusa ?asar nan cikin ya?i da bala’in ta’addanci, ‘yan bindiga, kidinafin, rashin zuwan yara makaranta da kuma shaye-shayen muggan ?wayoyi.

Ya ?ara da cewa wannan jerin ?alubalen ya samu ne sakamakon fatara da kuma rashin cigaban al’umma.

A cewar Yelwa, gwamnati a dukkan matakai ta na yin iyakar ?o?arin ta domin ta da?ile wa?annan matsalolin saboda ta daidaita komai.

Ya ce an ?auki matakai iri-iri, sannan an sawo sababbin kayan ya?i na zamani wa?anda aka sanya cikin ya?in.

Ya ce: “A kullum mu na fuskantar muggan abubuwan da wa?annan illoli su ke haifarwa a kan mutanen mu. A kullum ‘yan rahoton mu su na aiko da labaran hare-haren da ake kai wa ?auyuka ana fatattaka su, sannan ana kama mutane ana garkuwa da su.

“A kullum mu na bada labaran yadda mahara ‘yan bindiga ke aika wasi?u zuwa ga ?auyuka da al’ummomi su na cewa a kai masu ku?in fansa ko ku?in neman izinin zuwa gonakin su. Mu kan ji yadda ake harbe mutanen da aka sace idan an kasa biyan ku?in da za a ‘yanto su. Mu kan ji yadda gwamnoni su ke bayyana ba?in cikin su ko yadda yanzu wasu sassa na jihohin su ba su ?ar?ashin ikon su. Mu kan bada rahoto kan mutanen da a da su ke iya ciyar da kan su amma yanzu sun koma zaman dirshan a sansanin ‘yan gudun hijira.

“Kafafen ya?a labarai na Arewa su na kan gaba wajen kawo rahotanni game da wa?annan matsaloli. Hasali ma dai wasu daga cikin membobin ?ungiyar mu sun sha wuyar wannan hali da ake ciki na ta’addanci, a yayin da a kullum mu ke fa?akarwa kan a kyautata wa maya?an mu da kuma wa?anda rashin tsaron ya shafa. Za mu ci gaba da sauke nauyin mu na tabbatar da nuna wa gwamnati abin da ya dace ta yi, tare da bada dama ga duk wani mai son ya fa?i ra’ayin sa kan yadda za a samo mafita kan tabbatar da tsaro a Arewa da Nijeriya baki ?aya.”

Daga nan shugaban ?ungiyar ya bada sanarwar cewa daga yanzu sun ?aura ya?in fa?akar da jama’a kan wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Arewa. 

Yelwa ya ce, “A ci gaba da ?o?arin da ake yi na ya?i da rashin tsaro tare da bada gudunmawa ga nemo hanyoyin da za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da arzi?i a yankin mu da ?asar mu, ?ungiyar mu ta NMBOA ta na sanar da jama’a cewa ta fara yekuwa ta kafofin ta a kan wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar al’ummar mu. 

“Tsarin da za mu bi shi ne za mu yi amfani da inda mu ke shiga da fita da kuma hanyoyi daban-daban da ke fa?in Arewa da ma wajen ta, mu yi magana da hukumomin gwamnati a dukkan matakai, tare da ?ungiyoyi masu zaman kan su, da sarakuna da shugabannin addini da muhimman masu ruwa da tsaki domin a samo ingantattun shawarwari na jama’a da yadda al’ummomi za su kasance su ne kan gaba wajen ya?i da rashin tsaro.

“Ta hanyar tsara wasu shirye-shirye na musamman a tsanake, da tallace-tallace na musamman, da sauran su, za a ilmantar da masu saurare kan rawar da ya kamata su taka da kuma yadda abin da su ka yi ko su ka kasa yi ya ke taimakawa wajen samar da wani sakamako a wannan ya?i kan rashin tsaro. Hakan ya kasance cigaba ne da ha??in jama’a da ya rataya a wuyan mu a matsayin mu na hu?u a jerin masu fa?a a ji a cikin al’umma.”

Related posts

Leave a Comment