Ba Da Tallafin Lantarki Ya Nuna Tinubu Mutum Ne Mai Tausayi – Ministan Labarai

IMG 20240407 WA0063

Ministan Ya?a Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki kashi 85 cikin 100 da gwamnatin Shugaban ?asa Bola Tinubu ke yi ya ?ara nuna gwamnatin a matsayin dimokira?iyya mai son jama’a.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a jawabin sa na bu?e Taron Ministoci Karo na 4 a Cibiyar ‘Yan Jaridu ta ?asa da ke Abuja.

Ministan ya ce: “A kwanan baya, Gwamnatin Tarayya ta fitar da wani tsari na cigaba a fannin samar da wutar lantarki, wanda ke da nufin bun?asa wadatar wutar lantarki ga ?aukacin ‘yan Nijeriya.

“Wani muhimmin al’amari na wannan tsarin shi ne gwamnatin Tinubu na ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ga kashi 85 na masu amfani da wutar lantarki a Nijeriya, wanda hakan ya sake tabbatar da matsayin gwamnatin dimokaradiyya mai son jama’a tare da yin ?arin ku?in wutar lantarki ga kashi 15 na masu amfani da wutar lantarki kawai.”

Tun da farko, Ministan ya bayyana nasarorin da gwamnatin Shugaban ?asa Tinubu ta samu a baya-bayan nan. A cewar Idris, “Tun bayan ganawar da muka yi da ku (’yan jarida) na baya-bayan nan an samu gagarumar nasara a tattalin arzi?inmu, kasancewar dukkanmu shaida ne kan yadda ta hanyar aiwatar da wasu sauye-sauye na tattalin arzi?i, kasuwar canjin ku?a?en ?asar waje ta daidaita, sannan kuma naira yana samun ?arfi kullum.

“Kafa Majalisar Daidaita Tattalin Arzi?i da Tawagar Gudanar da Tattalin Arzi?i na Shugaban ?asa na kwanan nan ya jaddada ?udirin Shugaban ?asa don samar da wani tsari mai muhimmanci na gudanar da tattalin arzi?i wanda ke yin amfani da ?warewa da fahimtar manyan masu ruwa da tsaki daga ?angarorin gwamnati da masu zaman kansu. Wa?annan ?ungiyoyin za su zama dandamali don tattaunawa mai ?arfi, bincike, da yanke shawara don ha?aka ci gaban tattalin arzi?i mai ?orewa, samar da ayyukan yi, da wadata ga dukkan ‘yan Nijeriya.

“?addamar da Asusun Raya Gine-gine na Sabunta Fata (RHIDF) yana da niyyar tara kusan naira tiriliyan 20 don saka hannun jari a sassa masu muhimmanci kamar su tattalin arzi?i, sufuri, noma, da Fasahar Sadarwar Bayanai (ICT) da sauransu.

“Asusun yana neman tallafawa ayyukan da ke ha?aka ci gaba, samar da guraben aikin yi, da ha?aka fitar da kayayyaki zuwa ketare.”

Idris ya ?ara da cewa, “Ayyukan da asusun zai sa a gaba sun ha?a da gina babbar hanyar Legas zuwa Calabar da aka fara kwanan nan, titin Sokoto zuwa Badagry, Legas zuwa Kano, hanyar jirgin ?asa na Gabas da zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da na jiragen sama a fa?in ?asar.

“Don fa?a?a hanyoyin samun ilimi a matsayin makamin ya?i da talauci, Shugaban ?asa ya sanya hannu kan ?udirin dokar Lamunin ?alibai ta 2015, ta zama doka. Wannan yun?urin ya wuce doka kawai – hanya ce ta juyin juya hali don kafa tsari na dindindin wanda zai tallafa wa neman ilimi daga matasanmu.

Related posts

Leave a Comment