Zariya: Dakataccen Hakimi Ya Nesanta Kanshi Da Gayyatar ‘Yan Tauri

Daya daga cikin hakimai hu?u da mai martaba sarkin Zazzau ya dakatar daga hawan daba Honarabul Suleiman Ibrahim Dabo Wakilin Birnin Zazzau, ya bayyana cewa akasi aka samu a lokacin da tawagar mahayansa suka zo wucewa gaban sarki a lokacin hawan sallah.

Da yake tartaunawa da manema labarai Dabo ya ce bashi ne da kansa yayi hawa ba bana wakilin sa ne yayi hawa kuma babu yan tauri a cikin tawagar.

” Ko da tawaga ta suka taso tun daga gida basu tare da ‘?an tauri, na saka a ?auki bidiyon wannan hawa tun daga gida.

” Abinda ya auku shine a lokacin da tawaga ta suka iso kofa kafin su kai gaban sarki su wuce sai wasu ?an tauri da bamu san su ba suka yi wuf suka shiga gaban tawagar suka rika wasa da wukake a gaban sarki. Amma ba mu ne muka yo gayyan su ba.

Related posts

Leave a Comment