Muna Alfahari Da Zaman Lafiya Da Girmama Masarautu – Sarkin Bauchi

Daga Adamu Shehu Bauchi

Mai Martaba Sarkin Bauchi Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu yace suna alfahari tare da goyon bayan duk wani shugaba wanda yake kokarin tabbatar da zaman lafiya da kuma girmama masarautun gargajiya tare da yunkurin gina ababen more rayuwar al’umma a Najeriya

Sarkin yayi wannan furucin ne a cikin jawabinsa na Sallah karama yayin gudanar da bikin Hauwan Daushe da aka saba yi a kowace shekara a fadar gwamnatin Jihar Bauchi.

Mai Martaba Sulaiman Adamu a jawabinsa yace hakika babu shakka dole ne sai an samar da tsaro da wanzar da zaman lafiya kafin a samu al’umma mai inganci da zamantakewar rayuwa

Sarkin ya kara da cewa dawo da martaban masarautun gargajiya yana da matukar muhimmanci kwarai idan akayi la’akari da irin gudunmuwar da suke bada wa ta wajen wayar da kan al’umma akan zaman lafiya da kaunar juna, wanda yace hakan na samar da cigaba da kuma ba Gwamnati zarafin aiwatar da ayyukan da zai shafi talakan Nijeriya.

Yace kaman ayyukan gona da kirkiro masana’antu don rage zaman kashe wando da matasa ke yi a Jihar da ma kasa baki daya.

Sarkin ya yaba ma Gwamnan jihar Bala Mohammed kan jajircewarsa na ayyukan na al’umma tare da dakile duk wata fitina dake kokarin kunnu kai a fadin Jihar, yace abin a yaba masa ne.

Yace sarakuna za su cigaba da taimakon gwamnatin Bala Mohammed da gayon baya da duk wata dama da suke da ita domin a gudu tare a tsira tare,

Anashi jawabin Gwamnan jihar Bala Mohammed Kauran Bauchi yace zasu tabbatar da sun bama kowa dama a fagen siyasa domin adalci da zaman lafiyan jihar, musamman adaidai lokacin da ake shirin shiga zaben 2023 a Najeriya baki daya.

Related posts

Leave a Comment