Borno: Kungiyoyi Sun Damka Wa Zulum Miliyan 50 Na Sayen Fom

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar sama da kungiyoyi 179 ne suka tattara kudade suka gabatar da cakin kudi na Naira miliyan 50 ga gwamnan jihar Zulum domin sayen fom na takara a karkashin jam’iyyar APC.

Da yake gabatar da takardar kudi naira miliyan 50, kakakin Kungiyoyin, Alhaji Awaji Bukar, ya ce gudunmawar, wanda wasu daga cikinsu sun fito ne daga kasa da Naira 1,000 da wasu mambobinsu suka bayar, da nufin mika godiyarsu ga Gwamna Zulum bisa kyakkyawan jagoranci da ya yiwa al’ummar jihar Borno.

Ya yi bayanin cewa tallafin ya fito ne daga dimbin ma’aikatan da suka yi rajista na kungiyoyi sama da 179 da kungiyoyi da kwararru a fadin jihar.

A nasa martanin, Zulum, ya nuna jin dadinsa da amincewar da kungiyoyin suka yi masa, ya kuma ce ya yaba da wadanda suka ba da Naira 1,000 daga dan kankanin dukiyarsu.

Gwamnan ya tabbatar wa kungiyoyin da cewa idan aka zabe shi a karo na biyu gwamnatinsa za ta kara gina ababen more rayuwa da kuma zuba jari mai yawa a fannin kasuwanci, ilmin sana’a, ayyukan yi, samar da arziki da dai sauransu.

Related posts

Leave a Comment