Zargin Dauki Dora: APC Na Tafka Asara

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da ake sa ran APC za ta gudanar da taron majalisar zartarwar, wanda zai mayar da hankali wajen tattaunawa a kan shirin gudanar da zaben fitar da gwani domin tunkarar zaben 2023, wasu ‘yan jam’iyyar sun soma ficewa zuwa wasu jam`iyyu sakamakon zargin ana musu dauki-dora.

Barrister Soloman Dalong, tsohon Ministan Wasanni, kuma dan ga-ni-kashe-nin jam`iyyar APC, na daga cikin wadanda ke wannan zargi in da har ya shaida wa BBC cewa shi da APC fa haihata-haihata, har ma ya samu masauki a jam`iyyar SDP.

Dalong ya ce “Abin da ya sa muka kafa jam’iyyar APC shi ne kama-karyar da ake a jam’iyarmu ta da, da kuma nada mutane a kan mukamai da baba-kere, shi ya sa muka fice daga waccan jam’iyyar muka kafa APC, to kuma sai ga shi a kwana a tashi a ita jam’iyyar APC ma mun fara fuskantar waccar matsala.”

Ya ce “Babu wanda zai ce maka komai sai kawai wadansu su je su zauna a daki su nada shugabannin jam’iyya, shi ya sa na ga bai kamata na ci gaba da zama ba a jam’iyyar APC ba.”

Bayan tsohon Ministan Wasannin, akwai wasu Sanatoci da wasu jiga-jigan jam`iyyar da suka sauya sheka ko kuma suna kan hanyar yin hijira daga jam`iyyar APC irin su tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari.

Wannan lamari dai ya sa wasu `ya`yan jam`iyyar sun fara kira ga kwamitin zartarwar da ya dauki matakin gyara, idan ba haka to wankin-hula ka iya kai jam`iyyar dare.

Alhaji Abdurrahman Buba Kwacham, jigon APC ne a jihar Adamawa, ya shaida wa BBC cewa dole a yi hattara wajen barin shugabannin jam’iyya su zabi ‘yan takara wadanda suka dace da al’umma kuma suke so.

Ya ce “Maganar dauki-dora, to talakawan Najeriya ba za su amince da ita ba a yanzu ba, sannan yana da kyau shugabanni su fahimci cewa babu Buhari a zaben 2023, yanzu kowa da jam’iyya ne da sunansa da darajarsa da kuma abin da ya aikatawa al’umma.”

Alhaji Abdurrahman Kwacham ya ce,” Don haka yanzu mutane ba jam’iyya suke nema su zaba ba, a’a suna nema su zabi mutane ne.”

Masana siyasa dai sun sha hasashen cewa za a kawo gabar da jam`iyyar APC za ta kure hakurin wasu `ya`yanta.

Shugabannin jam`iyyar APC dai kan bayyana cewa duk wata jam`iyyar da ta bunkasa ba a raba ta da rikici, ballantana irin ta jam`iyya mai mulkin kasa.

Sun kuma ce suna da yakinin za su iya shawo kan kowanne irin rikicin cikin gida.

Related posts

Leave a Comment