Tinubu Ya Soki Lamirin Buhari Da Shugabannin Baya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar shugaban kasa Bola Tinubu ya soki shugabannin Najeriya masu ci da na baya, yana cewa zai magance matsalolin da suka kasa magancewa idan aka zabe shi shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a gaban wasu daruruwan matasa da suka taru domin nuna goyon bayansu a gareshi.

“Muna sane da fushinku. ban ga laifinku ba, alkawuran da aka sha yi muku a baya sun kasa biyan bukatunku, tun daga lokacin da kuke makarantar firamare. Ba za mu ci gaba da halayya irin ta da ba.”

Tinubu bai bambanta tsakanin gwamnati mai-ci ta Buhari ba da ta shugabannin da ya gada.

Related posts

Leave a Comment