Afuwa Ga Barayin Gwamnati: Buhari Ya Yi Karan Tsaye – Naja’atu Mohammed

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar fitacciyar ‘yar gwagwarmayar siyasar nan daga Jihar Kano Hajiya Naja’atu Mohammed, ta caccaki Shugaban Kasa Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba da ya yi.

Rahotanni sun bayyana yadda a ranar Alhamis, majalisar zartarwa wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

A wata tattaunawa da Radio France International, RFI a ranar Litinin, Naja’atu Mohammed ta ce ya dace Buhari ya gane cewa dukiyar Najeriya ba ta shi bace. A jiharsu ya dace a yafe musu in ji ta.

A cewarta, ya kamata gwamnonin jihohinsu su yafe musu ne, saboda a can suka aikata rashawar, don kundin tsarin mulki ya bayar da yafiya ne ga jihohin da aka aikata laifuka.

Ta kara da cewa yafe wa tsofaffin gwamnonin yana nuna cewa ba a shirya kawo karshen rashawar Najeriya ba. Ta ce kotu ta tabbatar da zargin da ake musu don haka yafiyar na nuna cewa ba a yaki da rashawa a kasar nan. A cewarta:

“Gwamnati ta yi kuskure. Ya dace shugaban kasa ya gane cewa dukiyar al’umma ba ta shi bace. Gwamnatin tarayya ba ta da damar yafe wa wadanda suka tafka laifi a jihohinsu. “Abu na biyu shi ne wannan yafiyar ta Buhari tana nuna cewa gwamnati ta gaza. Wannan shiyasa muke fama da rashin tsaro.

“Bayan EFCC da kotu sun gama iyakar kokarinsu tsawon shekaru, bai dace kawai ka yafe wa masu laifin ba. Ba kudinka suka sata ba. Me yasa gwamnatin Buhari ta ke yin yadda ta ga dama?”

Related posts

Leave a Comment