Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa Abba Kyari dake fuskantar gurfana a Kotun Gundumar California ta Amurka bisa zarginsa da hannu a wata damfara ta shahararren dan damfara, Ramon Abbas (Hushpuppi), na iya samun sassaucin hukunci daga hukuma.
Abba Kyari, wanda ya kasance mataimakin kwamishinan ‘yan sanda kuma shugaban shugaban wata rundunar fikira ta IRT a Najeriya. An dakatar da Abba Kyari yayin da aka fara gudanar bincike kan lamurran da suka faru tsakaninsa da Hushpuppi.
Bincike ya bayyana cewa, ana kyautata zaton Kyari ba zai dawo aikin dan sanda ba, amma zai iya samun sassaucin hukunci daga hukumomi, wanda daga cikin sassaucin shine; hukumar ‘yan sanda ba za ta mika shi ga hukumomin kasar Amurka ba.
An ruwaito cewa yayin da akwai kwararan alamu na cewa Sufeto Janar na ‘yan sanda (IG) na iya bayar da shawarar a sauke Kyari daga mukamansa, Hukumar Kula da harkokin ‘Yan sanda PSC za ta zabi sallamarsa gaba daya saboda girman laifin nuna rashin da’a ga aikin ‘yan sanda.
Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (DIG) Joseph Egbunike ya jagoranci kwamitin da IG ya kafa don binciken zargin da aka yi wa Kyari, a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta ya mika rahotonsa ga IG, Usman Baba. An kafa kwamitin ne a ranar 2 ga Agusta, 2021.
Kafa kwamitin ya biyo bayan gurfanar da Kyari a wata karar da ta shafi Hushpuppi, wanda ke da hannu a damfarar $1.1m kan wani dan kasuwa na kasar Qatar a Kotun Gundumar Amurka ta California.
An tattaro cewa hukumomin da abin ya shafa suna shirin baiwa jami’in da aka gurfanar sassauncin hukunci. Akwai kuma kungiyoyin goyon baya daga arewa dake kare Kyari. Hakazalika akwai lauyoyi da dama daga Arewa da suka bayyana kudurin kare Kyari a kotu.
An kuma tattara cewa IG, wanda da farko aka umarce shi da ya dakatar da Kyari tare da bincikar zarge-zargen da ake yi masa, kwanan nan ya sami karin umarni kan matakan da za a bi kan lamarin bayan gabatar da rahoton.
Bayan karbar rahoton, wasu majiyoyi daga hukumar ‘yan sanda sun bayyana a karshen mako cewa: “Suna iya yi masa sassaucin hukunci amma da alama ba zai koma aikin dan sanda ba. Hakanan akwai yuwuwar ba da izinin diflomasiyya don ba shi kariya.
