Matsalar Tsaro: Matasan Arewa Sun Roki Babangida Da Obasanjo Su Taimaka

Kungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NYLF), wadda ta ?unshi gamayyar kungiyoyin Arewa 42, ta yi kira ga tsofaffin shugabannin kasa Babangida da Obasanjo da su gaggauta kiran taron “Iyayen Najeriya” da nufin shiga tsakani a matsalolin kasar da kuma samar da mafita.

LKungiyar musamman ta yi kira ga Obasanjo da ya shiga tsakani a rikicin da ke kara ta’azzara a jam’iyyar PDP, tare da bayyana cewa jam’iyyar ita ce kadai fata ga ‘yan Najeriya, na fita daga halin da suke ciki.

?ungiyar ta kuma bayyana Obasanjo a matsayin “gogaggen dan kasa wanda ya yi imani da gamayyar Najeriya.” Shugaban NYLF na kasa, Elliot Afiyo, ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abeokuta, jihar Ogun, jim kadan bayan ganawarsu da Obasanjo.

Afiyo, wanda ya ambaci wasu ‘Iyayen Najeriya’ da suka hada da tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya), Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya) da Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) da Ernest Shonekan a matsayin wadanda ya kamata a nemi shawarwarin domin fita daga halin da ?asa ke ciki.

Kungiyar ta lissafo matasalolin Najeriya da suka ha?a da ‘yan bindiga, yawan garkuwa da mutane, cin hanci da rashawa, barakar tattalin arziki, tashe-tashen hankula daga ‘yan aware da dai sauran matsalolin da sauka dabaibaye kasar.

Ya ce lokaci ya yi da wadannan “‘yan Najeriya masu kishin kasa” za su hadu su kuma samar da mafita ga kalubalen da ake fuskanta kafin su dulmuye kasar.

Related posts

Leave a Comment