Taron gwamnonin da ya gudana a Kaduna ya kuma jinjinawa gwamnatin tarayya a kan sabbin matakan da take dauka wajen samun nasarar yakin da ake yi da ta’addanci da kuma ‘yan bindiga tare da masu garkuwa da mutane.
Yayin mahawara a kan yanayin da yankin arewacin Najeriya ke ciki, gwamnonin sun sake daga muryar su a kan barazanar da ake fuskanta na samun miliyoyin yaran da basa zuwa makaranta, abinda ya sa suka yanke hukuncin kara zuba kudade wajen samar da ingantaccen ilimi da sana’oi da kula da lafiyar al’umma da kuma samar da kayan more rayuwa.
Lura da illar da sauyin yanayi ke yiwa yankin, gwamnonin sun yanke hukuncin zuba jari domin bunkasa noma da samar da abinci tare da kare muhalli daga matsalolin da ake fuskanta ta hanyar da za’a taimakawa rayuwar al’umma.
Sanarwar bayan taron gwamnonin da ya gudana a karkashin shugabancin gwamnan Gombe, Alhaji Inuwa Yahya yace sun karbi rahoto a kan shirin bunkasa ilimin matan dake gudana a wasu jihohin arewacin Najeriya da ake kira AGILE wanda ke gudana da tallafin Bankin Duniya, inda suka bayyana gamsuwa da tasirin shirin da kuma alkawarin bada gudumawar da ake bukata daga nasu bangaren.
Taron gwamnonin ya kuma karbi tawagar shugaban kungiyar tintiba ta arewacin Najeriya da ake kira ACF, inda bangarorin biyu suka yanke hukuncin yin aiki tare da kuma magana da murya guda domin kare muradun yankin.
