Zan Warware Matsalolin Najeriya Idan Na Haye Karagar Mulki – Tinubu

?an takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya yi alwashin magance matsalolin da ke damun kasar idan ya samu nasarar karbar mulki a babban zaben da ke tafe.

A ranar talata nee ?an takarar ya kaddamar da yakin neman zaben nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda Shugaba Buhari da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka halarta.

Bola Tinubu ya lissafa mafi yawan matsalolin da ke damun Najeriya, ciki har da ?arancin abubuwan more rayuwa, da dur?ushewar masana’antu, da rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Kana ya yi alwashin magance su ta hanyar ha?a ?wararru kuma gogaggu a cikin gwamnatinsa idan ya samu nasarar kafawa.

“Mu a jam’iyyar APC da yardar Allah mun yi wa ?an Najeriya alkawarin yin shugabanci nagari a karakashin wannan yun?uri na farfadowa ko sabunta fatan alheri a zu?atan al’umma, sakamakon goyon bayan da kuke ba mu”.

Kazalika, dan takarar shugaban kasar ya caccaki abokan hamayyarsa… musamman ma na jam’iyyun adawa da ke gaba-gaba, wani lokaci har da kiran suna yana gugar-zana, yana cewa ba su san hanya ba, ballantana su yi wa wani jagora.

Duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci wajen taron amma bai ce komai ba, face dan?awa ?an takarar tutar jam’iyya da ya yi.

An dai kammala taro ana ta annashuwa, amma wani su?ul-da-baka da dan takarar shugaban kasar ya yi ta janyo ce-ce-ku-ce, lokacin da zai yi fatan alheri ga jam’iyyar a karshen jawabinsa sai ya ?uge da ambaton sunan jam’iyyar adawa!
Sai dai nan take ya gyara.

Related posts

Leave a Comment