An ruwaito jihohin da rahoton ya yi hasashe sun ha?a da, Abiya, Adamawa, Bauchi, Benuwai, Borno, Kuros Riba, Edo, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, da Katsina. Sauran sune, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Filato, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe, da kuma jihar Zamfara.
A cewar rahoton ‘yan Najeriya miliyan 25.3 ake hasashen zasu shiga matsalar rashin abinci a jihohi 26 tsakanin watan Yuni da Agusta, 2023.
Daga cikin jihohin dake sahun gaba da yawan wa?anda matsalar zata shafa akwai Borno mai mutane miliyan 1.4m, Yobe da miliyan 1.3m da kuma Adamawa mai miliyan ?aya cif.
Rahoton ya kuma bayyana cewa kusan ‘yan Najeriya miliyan N17m ne ke fama da rashin abinci yanzu haka ciki harda ‘yan gudun Hijira da kuma wa?anda aka maida gidajensu. Haka nan rahoton yace mutane 41,000 wa?anda a halin yanzun suke fama da yunwa zasu shiga matsanancin yanayin rashin abinci daga cikin yan gudun Hijira 83,000 a jihohin Benuwai, Taraba da Kuros Riba.
A wannan lokacin da aka ?iba, cin abinci zai ragu sakamakon raguwar magidanta, da kayan abinci da kuma hauhawar farashin kayan abinci a kasuwanni.
?ungiyar kula da Abinci da noma ta majalisar ?inkin duniya (FAO) da wasu ?awayenta ne suka gudanar da wannan bincike karkashin jagorancin gwamnatin Najeriya ta hannun ma’aikatar noma da raya karkara.
Abubuwan da suka jawo rashin isasshen abinci Rahoton ya ayyana rashin tsaro, ambaliyar ruwa, hauhawar farashin kayan abinci, tashin farashin kayan noma da fa?uwar darajar Naira a matsayin manyan abubuwan da suka jawo ?alubalen.
