Zan Shafe Tarihin PDP Idan Na Zama Shugaban APC – Modu Sheriff

Tsohon Gwamnan Jihar Barno Ali Modu Sheriff ya ce babu mahalukin da ya yi wa jam’iyyar APC aiki tu?uru, tun farkon kafuwar ta, kamar shi.

Ya ce a matsayin sa na ?aya daga cikin jiga-jigan da suka kafa APC, babu abin da ke cikin sa da zuciyar sa kamar ganin cewa jam’iyyar ta bun?asa sosai.

Sheriff ya yi wannan bayani a wani taron manema labarai, ranar Juma’a, a Abuja.

Sheriff wanda tsohon sanata ne kafin ya mulki Barno, ya bayyana cewa zai fito takarar shugabancin APC na ?asa baki ?aya.

Duk da cewa jam’iyyar ba ta bayyana shiyyar da za ta dam?a wa takarar shugabancin jam’iyyar ba, amma dai za a yi Taron Gangamin Jam’iyya a ranar 26 Ga Fabrairu.

Sheriff wanda har Shugaban Jam’iyyar PDP na ?asa ya taba ri?ewa, ya ce a yanzu ya na so ne ya fito takarar shugabancin APC, idan aka dam?a shugabancin APC ?in ga ‘yan yankin Arewa maso Gabas.

Sannan kuma ya ce tuni har ma ya yi nisa da tuntubar manya, dangane da yadda za a yi wa APC garambawul domin fuskantar ?alubalen da ka iya yi wa APC karan-tsaye, bayan kammala wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki.

Related posts

Leave a Comment