Tsohon Gwamnan Jihar Barno Ali Modu Sheriff ya ce babu mahalukin da ya yi wa jamiyyar APC aiki tu?uru, tun farkon kafuwar ta, kamar shi.
Ya ce a matsayin sa na ?aya daga cikin jiga-jigan da suka kafa APC, babu abin da ke cikin sa da zuciyar sa kamar ganin cewa jamiyyar ta bun?asa sosai.
Sheriff ya yi wannan bayani a wani taron manema labarai, ranar Jumaa, a Abuja.
Sheriff wanda tsohon sanata ne kafin ya mulki Barno, ya bayyana cewa zai fito takarar shugabancin APC na ?asa baki ?aya.
Duk da cewa jamiyyar ba ta bayyana shiyyar da za ta dam?a wa takarar shugabancin jamiyyar ba, amma dai za a yi Taron Gangamin Jamiyya a ranar 26 Ga Fabrairu.
Sheriff wanda har Shugaban Jamiyyar PDP na ?asa ya taba ri?ewa, ya ce a yanzu ya na so ne ya fito takarar shugabancin APC, idan aka dam?a shugabancin APC ?in ga yan yankin Arewa maso Gabas.
Sannan kuma ya ce tuni har ma ya yi nisa da tuntubar manya, dangane da yadda za a yi wa APC garambawul domin fuskantar ?alubalen da ka iya yi wa APC karan-tsaye, bayan kammala waadin Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki.

