Abuja: An Shiga Rudani Biyo Bayan Kisan Da Wata Malama Ta Yi Wa Dalibi

Wata Malamar makarantar kwalejin tarayya Kwali, Dorcas Gibson, ta yiwa wani dalibi mai suna Yahaya Nuhu dukan da ya sanya yace ga garinku nan saboda bai yi aikin da ta bashi ba.

Daily Nigerian ta gano cewa makarantar suna neman rufe wannan lamari, inda suka danganta mutuwar yaron da zazzabin cizon sauro da ya kama dalibin inda suka kai shi asibiti.

Tuni makarantar sun kaiwa iyayen yaron takardun mutuwarshi, inda suka nuna musu cewa dalibin JSS 2 din mai shekaru 13 ya mutu sanadiyyar zazzabin cizon sauro.

Yahaya dai ya mutu ne a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, sakamakon buga masa hannun bokiti da Mrs Gibson ta yi a kan sshi.

Bayan makarantar sun gano cewa dalibin ya mutu ne sanadiyyar dukan da Malamar ta yi masa, cikin sauri suka garzaya da gawarshi zuwa asibitin makarantar daga nan kuma suka wuce dashi asibitin Rema don a yi rufa-rufa kan mutuwar shi.

Daily Nigerian ta gano cewa bayan hukumar makarantar ta sanar da iyayen yaron cewa ya mutu sanadiyyar zazzabin cizon sauro, iyayen sun dauki kaddara ba tare da zargin komai ba.

Sai dai kuma bayan kwana biyu da mutuwar Yahaya, lamari ya canja kan mutuwar Yahaya, a lokacin da ‘yan ajinsu suka je yiwa iyayenshi ta’aziyya.

A yadda ‘yan ajinsu suka bayyana, Yahaya ya sanar da Malamar halin da yake ciki dangane da aikin da ta bayar ta bukaci kowa ya kai mata.

Sakamakon wannan magana da ya yi mata, ya sanya ta ce yaje ya cire ciyawa a matsayin horo bisa abinda ya yi. Bayan ya kammala wannan aiki Malamar ta fara dukan shi har sai da ya mutu.

Mrs Gibson ta shigo ajin mu ta bukaci mu nuna mata aikin da ta bamu, ni da Yahaya bamu yi ba, sai ta ce muje mu cire ciyawa.

Yahaya ya sanar da Malamar cewa bashi da lafiya, hakan ya sanya bai yi aikin ba, duk da haka dai ta tura mu cirar ciyawa, inda bayan mun gama muka dawo aji.

Kanshi na kwance akan kujera saboda rashin lafiyar da yake yi, amma duk da haka ta dake shi, ta buga masa hannun bokitin karfe a kai, hakan ya yi sanadiyyar mutuwar shi.

Cewar daya daga cikin daliban

Daily Nigerian ta gano cewa bayan iyayen yaron sun tunkari makarantar kan wannan lamari, makarantar ta bukaci ganawa da su a ranar 11 da 13 ga watan Agusta, inda a karshe suka amince cewa Malamar ce ta kashe dalibin.

Wata majiya a wajen taron ta sanarwa da Daily Nigerian cewa hukumar makarantar ta roki iyayen yaran akan su yi hakuri su yafe wannan lamari, saboda idan aka kai lamarin gaba zai kawo rashin jin dadi.

Bayan tuntubar shi da Daily Nigerian ta yi dangane da wannan lamari, shugaban makarantar, Dahiru Shehu, bai amsa kiran wayar su ba.

Related posts

Leave a Comment