A ?o?arin ta na ganin an samu yawaitar masu jefa ?uri’a, ya zuwa yanzu, Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) ta samu bu?atar yin rajista guda 2,449,648 daga ranar da ta fara aikin rajistar masu za?e (wato Continuous Voter Registration, CVR) wato 28 ga Yuni, a cewar wani jadawalin mako-mako na aikin wanda aka fitar a ranar Litinin a Abuja.
Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa jadawalin ya kuma nuna cewa ya zuwa yanzu, ‘yan Nijeriya 1,923,725 ne su ka kammala matakan farko na yin rajistar su ta hanyar yanar gizo a cikin wannan lokacin na mako bakwai a daidai ?arfe 7 na safiyar ranar Litinin, 16 ga Agusta.
Bugu da ?ari, INEC ta kuma bayyana cewa ‘yan Nijeriya 315,791 ne su ka kammala rajistar su ta hanyar yanar gizo ko ta hanyar ido da ido a cibiyoyin yin rajista da ke fa?in ?asar nan, a cikin wannan tsakani tun da aka fara aikin.
Hukumar Za?en ta nuna cewa bu?atun yin rajista guda 2,449,64 da ta kar?a sun ha?a da masu son yin sauyin wurin za?e da masu son a sauya masu katin za?e (PVC) da masu son a gyara masu bayanan su da ke kan katin su na za?e, da sauran su.
A kan batun jinsi na masu bu?atar za?en su 2,449,64, al?aluman sun nuna cewa mutum 1,370,469 maza ne, yayin da 1,079,179 mata ne, sannan 28,789 na?asassu ne.
Wajen shekarun mutum kuma, al?aluman sun nuna cewa mutane 1,592,178 matasa ne ‘yan shekara tsakanin 18 zuwa 34, sannan mutum 585,802 masu tsaka-tsakin shekaru ne daga shekara 35 zuwa 49, yayin da mutum 238,606 wa?anda su ka manyanta ne, wato ‘yan shekara 50 zuwa 69, sannan kuma mutum 33,062 dattawa ne ‘yan shekara 70 zuwa sama.
Da aka dubi rabe-raben shekarun na mutum 315,791 da su ka kammala rajistar su, an gano cewa mutum 176,379 maza ne, yayin da mutum 139,412 mata ne; wanda daga ciki kuma mutum 3,554 mutane ne masu fama da wata na?asa.
Haka kuma aikin rajistar ya nuna cewa masu bu?atar rajista mutum 126,936 sun soma ne daga yanar gizo, yayin da masu bu?ata 188,855 su ka fara tare da kammala matakan rajistar su ido da ido a cibiyoyin rajista.
Rabe-raben rajistar ta fuskar sana’a ko aikin yi kuma ya nuna cewa mutum 19,041 masu sana’o’i ne, mutum 59,441 ‘yan kasuwa ne maza da mata, 17, 482 ma’aikatan gwamnati ne, sannan 20,682 kuma manoma ne ko masunta.
Sauran sun ha?a da matan aure 26,993, da mutum 17,347 ‘yan tireda, da 5,679 ma’aikatan gwamnati, da ?alibai 130,961, da kuma wasu 18,165 wa?anda ba a bayyana aikin su ba.
Daga jimillar mutane 1,923,725 da su ka kammala matakan rajista ta hanyar yanar gizo, Jihar Osun ce a kan gaba da mutum 346,819, yayin da Jihar Edo ke bi mata da mutum 179,422, sai Bayelsa da mutum 160,793, da kuma Jihar Delta da mutum 117,400.
Jihohi masu ?arancin masu yin rajista ta hanyar yanar gizo sun ha?a da Inugu da mutum 6,112, sai Borno da ke bi mata da mutum 6,328 da kuma Yobe da mutum 6,363.
