Bakanuwa Ta Lashe Gasar Sarauniyar Kyau

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Wata matashiya ‘yar asalin Jihar Kano Shatu Garko ta lashe Gasar Sarauniyar kyau ta kasar.

Shatu Garko, mai shekara 18, ta doke zaratan mata 18 a bikin da aka gudanar ranar Juma’a da dare a Landmark Centre da ke birnin Legas.

Shatu ce mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria a Turance.

Nicole Ikot ce ta zo ta biyu, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku a gasar wadda ta samu halartar manyan mutane a ciki da wajen ?asar.

Ta kar?e kambin ne daga hannun Etsanyi Tukura ‘yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43 a 2019.

A cewar masu shirya gasar, wadda ta yi nasara za ta samu kyautar ku?i naira miliyan 10, da zama a gidan alfarma na shekara ?aya, da sabuwar mota, da kuma zama jakadiya ta musamman ga wasu kamfanoni.

Masu kula da gasar sun ce ana samun sabbin al’amura a kowace shekara game da matan da ke fafatawa tsawon shekara 44 da ake gudanar da ita.

Wace ce Shatu Garko?

Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta 44, Shatu Garko ‘yar asalin Jihar Kano ce kuma ita ce ta wakilci yankin arewa maso yammacin ?asar.

Ta?aitaccen tarihinta da aka bayar a wurin gasar ya nuna cewa tana da shekara 18 da haihuwa, kuma mai tallan hijabi ce da ke ?aunar hawa doki.

Related posts

Leave a Comment