Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta samu nasarar da?ile hare-haren ‘yan bindiga a fa?in ?ananan hukumomin jihar guda hudu, tare da ku?utar da wasu mutum hu?u da aka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Shehu, ya fitar ya ce ‘yan bindigar sun yi ?o?arin kai hare-hare a wasu ?auyuka da ke ?ananan hukumomin Maru, da Bungudu, da Tsafe da kuma ?aramar hukumar Bukkuyum.

Ya ce jami’ansu sun samu nasarar da?ile hare-haren ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

SP Mohammed Shehu, ya ?ara da cewa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi sun samu bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan bindigar na shirin ?addamar da hare-hare tare da mutane a ?auyukan da ke wan?annan ?ananan hukumomi

Related posts

Leave a Comment