Matsalar Tsaro: Buhari Zai Yi Taron Gaggawa Da Shugabannin Tsaro

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai gudanar da taro na gaggawa da manyan hafsoshin tsaron ?asar, a ranar yau Litinin domin sake duba halin da tsaron ?asar ke ciki.

A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafafen yada labarai Malam Garba shehu ya fitar, ya ce a yayin ganawar shugaban ?asar zai saurari bayanai daga manyan hafsoshin tsaron, tare da ?ara ?aimi a fannonin da ke bu?atar kulawa.

A ‘yan kwanakin nan ne dai Ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya a Najeriya suka fitar da jerin garga?in cewa akwai barazanar kai hare-hare a wasu sasan ?asar, har ma da Abuja.

Tun bayan bayyanar rahoton jama’a da dama musamman mazauna birnin tarayya Abuja sun shiga damuwa da tashin hankali sakamakon halin fargaba da suka tsinci kansu ciki dalilin rahoton.

Related posts

Leave a Comment