Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya daga jihar su Shida wa?anda suka koma jam’iyyar APC tare da gwamna Matawalle sun yi amai sun lashe.
‘Yan majalisar wakilan sun sake komawa jam’iyyar PDP kuma sun kar?i tikitin takara a babban za?en 2023 ba tare da hamayya ba.
‘Yan majalisar sun sake komawa PDP ne sakamakon yarjejeniyar da aka yi yayin sulhun gwamna Bello Matawalle na Zamfara, tsohon gwamna Abdul-Aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa.
Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar APC ta hana yan majalisun damar siyan Fom ?in tsayawa takara a za?en 2023 saboda ta riga da ta ba wasu sabbi kujerun su.
‘Yan Majalisar da suka koma PDP ?in sun ha?a da, Honorabul Ahmad Maipalace na maza?ar Gusau/Tsafe, Honorabul Bello Hasan na maza?ar Shinkafi/Zurmi da Honorabul Sulaiman Gummi na maza?ar Gummi/Bukkuyum.
Sauran su ne; Honorabul Sani Umar na maza?ar Kaura-Namoda/Birnin Magaji, Honorabul Shehu Ahmad na maza?ar Maru/Bungudu, da kuma Honorabul Ahmad Muhammed mai wakiltar maza?ar Bakura/Maradun a majalisar tarayya.
