Kaduna: Isa Ashiru Ya Lashe Zaben Fidda Gwani A PDP

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsohon ?an majalisar wakilai mai wakiltar ?ananan hukumomin Ma?arfi da Kudan a majalisar wakilai Alhaji Isa Ashiru Kudan ya lashe za?en fidda gwani na jam’iyyar PDP da babban rinjaye.

Alkaluman sakamakon za?en sun nuna cewar Isa Ashiru Kudan ya samu kuri’u mafiya rinjaye inda ya doke abokan takarar shi da samun kuri’u 414.

Tuni wasu daga cikin abokanan takarar tashi suka amince da kayen har suka mi?a sakon taya shi murna bisa ga nasarar da ya samu.

Tuni tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa Sanata Shehu Sani wanda kuri’a biyu rak a za?en ya wallafa sakon taya murna ga Isa Ashiru Kudan da kuma mika godiya ga Deligates da suka za?e shi ba tare ya basu ko sisi ba.

Related posts

Leave a Comment