Kungiyar ‘yan Jarida ta ?asa reshen Jihar Kaduna ta yi kira da babbar murya ga jam’iyyar PDP da ta gargadi jami’in ya?a labarai na jam’iyyar a jihar Kaduna Katoh Alberah a ?o?arin da yake yi na raba kawunan ‘yan Jarida a jihar.
Kiran ya biyo bayan matakin da jami’in ya?a labaran ya ?auka na za?ar wasu ‘yan Jarida a matsayin wadanda za su yi rahoto a za?en fidda gwani na jam’iyyar da ke gudana a Kaduna da yin watsi da wasu ‘yan Jaridar.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba a Kaduna a taron karshen wata da kungiyar da ya gudana a Kaduna.
A cikin takardar bayan taron wadda ta samu sanya hannun Usman Sani ta bayyana matakin da Mista Katoh Alberah ke dauka a matsayin wani yunkuri na haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan Jarida a jihar.
Sanarwar ta bayyana jami’in ya?a labaran a matsayin Mutum mai ?agawa da nuna girman kai ga ‘yan Jarida a jihar.
Kungiyar ta shawarci ‘yan Jarida a jihar da su cigaba da gudanar da ayyukan su cikin tsari da ha?in kai da kauce wa dukkanin wani abu da zai kawo sa?ani a tsakanin su.
“Matu?ar Mista Katoh Alberah zai cigaba da yin hakan babu shakka ?ungiyar ba ta da wani za?i wanda ya wuce ta ?auracewa ?aukan labaran jam’iyyar PDP a Jihar.
Daga ?arshe ?ungiyar ta yi Allah wadai da cin zarafin da wasu jami’an tsaro suka yi wa ‘yan Jarida a yayin taron da Jam’iyyar PDP ta gudanar kwanan nan.
