Dubai: Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Sa Wa Najeriya Takunkumi

?asar Ha?a??iyar Daular Larabawa ta gindaya sabuwar dokar biza ga ‘yan Najeriya da ke son shiga kasar.

Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta ?asa ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Tuwita.

Wannan na zuwa ne bayan da wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda ‘yan kasar ke ragaita a filin jirgin saman Dubai bayan da aka hana su shiga kasar saboda sabuwar dokar biza da Dubai ta bullo da ita.

Sanarwar ta ce ”Ofishin jakadancin Najeriya da ke Dubai ya tabbatar musu da cewa, mafiya yawan mutanen sun je kasar ne da bizar iyali, bayan da kuma suka je ba tare da kowa daga cikin iyalan nasu ba, bisa wannan dalili ne aka hana su shiga kasar, inda aka umarce su da su koma Najeriya su sake neman wata bizar, to amma wadanda suka tabbatar da cewa iyalansu na kasar an bar su sun shiga, wadanda kuma suka yi ikirarin cewa iyalansu na cikin wasu jiragen da ke tafe, sai aka ce su zauna nan su jira isowar ‘yan uwan nasu”

Related posts

Leave a Comment