Rahotannin dake shigo mana daga jihar Borno na bayyana cewar Manyan kwamandojin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram/ISWAP tare da mayakansu da dama aka kashe, a wani gagarumin farmaki da sojojin kasa tare da hadin gwiwar sojojin saman kasar suka kaddamar.
Wata majiyar leken asiri ta tsaro ta shaidawa PRNigeria cewa, dakarun da ke karkashin Operation Hadin Kai, sun kaddamar da hare-haren ba zato ba tsammani daga bangarori daban-daban a gefen dajin Sambisa.
“Rundunar sojin Najeriya ce ta kaddamar da farmakin bayan da wasu bayanan sirri suka bayar da takamaiman wuraren da kwamandojin ‘yan ta’addan da sojojin da ke kafar su suke.
“Kafin a fara aikin, rundunar sojin sama ta tura manyan jiragen yaki da kuma Super Tucano domin samar da hanya ga sojin kasa.
“Dakarun kasa sun yi nasarar harba rokoki da aka auna kan maboyar kwamandojin da mayakansu.
