Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Majalisar Dokokin Jihar a ranar Laraba ta ka?a ?uri’a domin tsige mataimakin gwamnan jihar Barrista Mahdi Aliyu Gusau.
Rahotanni sun bayyana cewa ?an majalisa 20 cikin 24 sun za?i a tsige mataimakin gwamnan bayan wani rahoto da kwamitin shari’a a jihar ya gabatar a kansa da ya same shi laifi kan zarge-zargen da ake yi masa.
?aya daga cikin ?an majalisar da suka halarci zaman Honarabul Ibrahim Tudu Tukur mai wakiltar Bakura ya tabbatar wa manema labarai cewa su 21 cikin 24 suka halarci zaman kuma mutum 20 sun amince da a tsige mataimakin gwamnan.
Tsigewar ta biyo bayan amincewa da rahoton da wani kwamitin bincike da ya binciki zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan na saba ka’idar aiki ya mika.
