Wata kotu a birnin Paris ta yanke hukuncin daurin gyara halinka na tsawon watanni hudu zuwa shida ga wasu mutum 11, bayan samun su da laifin “muzguna wa” wata matashiya a shafin intanet.
Matashiyar wadda yar ma?igo ce ta ri?a wallafa bidiyon ?atanci na addinin Musulunci a kafofin sada zumunta bayan da aka rika zaginta a intanet game da yadda take rayuwa.
Haka kuma matashiyar da ake kira Mira ta ri?a fuskantar barazanar mutuwa bayan da bidiyon ya bayyana a kafofin sada zumunta.
Lamarin ya zama wata alama da ke nuni da rigimar da ake yi a kan ?ancin tofa albarkin baki da addini a kasar ta Faransa.
Ya kuma ce sai da Miss Mila ta sauya gidan da take zama da makaranta don tsaron lafiyarta, kuma kuma an ba ta ?an sanda domin su ba ta kariya.
