Zai Yi Wahala Jama’ar Borno Su Amince Da Tubabbun Boko Haram – Shehun Borno

Rahotanni daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na bayyana cewar Shugabannin gargajiya da na addini a Borno sun ce zai yi wahala a sake karbar ‘yan Boko Haram da suka tuba cikin garuruwa su.

Shugabannin sun bayyana fargaba kan yadda sojojin Najeriya za su raba tubabbun ‘yan Boko Haram da tsattsauran ra’ayi a karkashin shirin su na Safe Corridor, domin dawo dasu cikin al’umma.

Da yake magana a madadin shugabannin sarakunan gargajiya na jihar mai Martaba Shehun Borno ya ce ba za su taba mantawa da barnar da Boko Haram tayi masu ba a Daular Borno.

Shehun Borno Abubakar El-Kanemi, ya ce matakin mika wuya da tubabbun Boko Haram din suka yi abu ne mai kyau amma mutane za su ci gaba da kasancewa cikin fargaba na bala’in tashin hankalin da aka shafe shekaru 12 ana yi, musamman mazauna garuruwan da za a mayar da masu tayar da kayar bayan.

“Shirin Safe Corridor na Sojoji ya kai ga kawar da tsattsauran ra’ayin tubabbun ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas. Amma zai yi matukar wahala mu sake karbar tubabbun ‘yan ta’addan cikin garuruwanmu da aka lalata.”

Ya kara da cewa Boko Haram sun lalata garin Bama da kwalejin ilimi a watan Satumba, 2014. An ruwaito cewa maharan sun kashe hakimai 13 da masu unguwanni da dama a kananan hukumomi 16 na Borno.

Shehun Borno ya kara da cewa: “Abu ne mai sauki a gafartawa asarar rayuka da dukiyoyi da yawa, amma yana da wahala a manta da asarar rayuka a cikin garuruwa daban -daban na Masarauta ta.

“An kashe mutane da yawa tare da kadarorinsu na tsawon shekaru 12. Kuma ku mutane da kafafen watsa labarai kuna sanya ran mu manta sannan kuma mu yafe wa ‘yan ta’adda da suka tuba? ”

Related posts

Leave a Comment