Kisan Bayin Allah: Masari Ya Sha Alwashin Maka Hukumar Kwastam Kotu

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar biyo bayan kisan da aka yi wa mazauna garin guda 10 yayin aikin atisaye kan iyaka a yankin Jibia na jihar Katsina, Gwamna Aminu Bello Masari, ya yi barazanar daukar matakin shari’a kan hukumar kwastam ta Najeriya (NCS).

A cikin wata sanarwa daga babban daraktan yada labaransa, Abdulabaran Malumfashi, yayi Allah wadai da yawan kashe-kashen mazauna jihar da hukumar NCS ke yi.

Masari ya bayyana cewa daga yanzu gwamnatinsa ba za ta sake lamunta da irin wannan lamari ba. Ba za a lamunci kashe-kashen mutane da basu ji ba basu gani ba a Katsina Sanarwar ta ce.

“Gwamnan ya yi Allah-wadai da kashe-kashen rashin hankali da ake yi wa ‘yan kasa ta hanyar tukin ganganci daga jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya. “Gwamnati na duba yiwuwar daukar matakin doka a kan Hukumar Kwastam ta Najeriya domin hana aukuwar wadannan munanan abubuwan da ke faruwa a cikin jihar.”

An ruwaito cewamatsayin Masari ya samo asali ne daga kisan mutane takwas da aka yi kwanan nan, wanda ya haura zuwa 10, wanda jami’an kwastam da ke atisayen kan iyaka a karamar hukumar Jibia suka bi ta kansu a ranar Litinin, 9 ga Agusta, 2021.

Related posts

Leave a Comment