Kimanin gidaje dari da saba’in ne 170 da gonaki masu yawan gaske akayi asara, a sanadin ambaliyan ruwan sama da aka sheka kamar da bakin kwarya a yankin Cheledi cikin karamar hukumar Kirfi a Jihar Bauchi,
Gwamnan Jihar Bala Abdulkadir Muhammed ya kai ziyarar ganin irin barnan da ambaliyar ruwan ta haifar a yankin, kana Gwamnan yayi alkawarin kai masu kayan dauki domin rage dumbin asarar da suka yi, kana ya kara da cewa ankai masu tireloli biyu na abinci (Masara da Shinkafa) a mazaunin somin tabi.
Bala yace, “zamu kafa kwamitin gaggawa damu da Yan majalisan dokokin jiha, domin tantance yawan asarar da akayi, ya kuma ce, zamu gayama Gwamnati tarayya don a tallafa ma mutanen yankin, domin wan nan asarace da take da bukatar hada karfi da karfi domin rage ma wadanda suka tafka asara radadi”
“Munsan Shugaban kasa mutumnne na talakawa, saboda haka munsan gwamnatin tarayya zata yi nasu hanyar da ta tashi daga Cheledi zuwa garin Gombe Abba daya hada mutanen yankin da na Jihar Gombe” Gwamnan ya fada.
Da yake janjanta ma mutanen yankin wadanda suka samu mafaka a wata makarantar primari a garin cheledin, ya gargadi mutanen da su guji aika fasadi a wurin matattaran da suka samu kansu domin akwa bata gari, a cikin al’umma wadanda ba asansu ba, kana yaja hankalinsu da su kula da tsaftace wurin da Kuma wanke hannu a koda yaushe don kaucewa cutar amai da godawa.
Malam Yusuf Yana daya daga cikin wadanda suka rasa gidansu gaba daya, yace yana rokon Gwamna da yasa mutane masu adalci wajen rabon kayan tallafi in an kawo, saboda anshayin haka a wasu wurare kana daga baya Kari kajin sunyi yadda suke so da kayan tallafin, rokonmu kenan a halin yanzu, Kuma wan nan Ibtila’i Allah ne ya kawo mana.
Kana mutanen garin sun tabbatar ma da manema labarai cewa ba asamu rasa rayuka ba duk da dumbin asarar da akayi a sanadin ambaliyan ruwan a yankin Cheledi a karamar hukuma ta Kirfin.
Daga Adamu Shehu Bauchi
