Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhamadu Buhari, ya yi wa za?a??en gwamnan Jihar Ekiti a ?ar?ashin Jam’iyyar APC murnar lashe za?en gwamnan jihar.
A wani sa?on da Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bu?aci duka ?an Jam’iyar APC a ciki da wajen Najeriya da su kalli wannan za?en a matsayin manuniyar nasarar APC a za?en 2023.
Shugaba Buhari ya yaba wa Biodun Oyebanji kan nasarar da ya samu a za?en inda ya ce ya cancanci ya zama gwamna sakamakon irin gudunmawar da ya bayar wurin kawo ci gaba a Jihar Ekiti da kuma Jam’iyyar APC a jihar tun kafin ya zama ?an takara.
A ranar Asabar ne dai aka gudanar da za?en Jihar Ekiti inda Biodun Oyebanji ya lashe za?en da ?uri’a 187,057.
