Kano: NNPP Ta Maye Gurbin Shekarau Da Rufa’i Hanga A Takarar Sanata

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Jam’iyyar hamayya ta NNPP mai alamar kayan marmari, ta tsaida wanda zai yi mata takarar Sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2023 bayan ficewar Shekarau daga jam’iyyar.

Ibrahim Adam wanda yana cikin hadiman jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya tabbatar da wannan a shafin Facebook. Malam Adam ya daura hoton Rufai Hanga a yammacin Alhamis, 8 ga watan Satumba 2022, inda ya yi masa take da cewa ‘Mai girma Sanata’.

Wannan ya yi nuni da cewa Sanata Rufai Hanga ne wanda jam’iyyar adawa ta NNPP ta ba takaran ‘dan majalisa na yankin tsakiyar Kano biyo bayan taron da shugabannin NNPP na tsakiyar Kano suka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke titin Madobi, inda suka tabbatar da takarar.

Related posts

Leave a Comment