Yobe: Sunan Shugaban Majalisa Ya Bayyana A Jadawalin INEC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa an bayyana sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na jam’iyyar APC a zaben 2023.

Lamarin na zuwa ne ‘yan awanni bayan Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar, ya jadadda cewa ba zai janyewa shugaban majalisar dattawan ba.

Lawan dai ya yi takarar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar APC sannan awanni kafin fara zaben fidda gwanin sai shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sanar da shi a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar.

Daga baya Sanatan ya sha ?asa a hannun jagoran APC na Kasa Bola Tinubu wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Related posts

Leave a Comment