Zaben Adamawa: Kotu Ta Kori Karar Aisha Binani

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ?arar da ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa ?ar?ashin jam’iyyar APC Sanator Aisha Ahmed Binani, ta shigar gabanta tana neman kotun ta tabbatar da ita a matsayin wadda ta yi nasara a za?en da aka kammala ranar 15 ga watan Afrilu.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi fatali da ?arar bayan da ya fahimci cewa mai shigar da ?arar ta nemi ta janye ?orafin nata.

Duk da cewa lauyanta Mohammed Sheriff ya shigar da bu?atar janyewa daga ?arar, mai shari’a Ekwo ya ?i amincewa da bu?atar janyewar, yana mai cewa korar ?arar shi ne abin da ya dace.

Saboda a cewarsa tun da farko kotun ta bu?aci mai shigar da ?arar ta yi wa mata bayanin dalilanta na shigar da ?arar.

Tun da farko Sanator Binani ta je kotun ne da nufin bu?atar kotun ta dakarar da hukumar za?en ?asar INEC da ayyana kowa a matsayin wanda ya yi nasarar a za?en gwamnan jihar, bayan kwamishin za?en jihar Hudu Ari ya ayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara.

A cikin ?orafin da ta shigar, ‘yar takarar jam’iyyar APCn ta dage cewa ita aka bayyana a matsayin wadda ta lashe za?en gwamnan jihar Adamawa da aka kammala ranar 15 ga watan Afrilu.

Ta ce INEC ba ta da hurumin soke ko sake ayyana wani ?an takarar bayan jami’in hukumar ya ayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara.

Related posts

Leave a Comment