Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar za?a??en shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya koma gidan da kundin tsarin mulkin ?asa ya tanadar wa za?a??en shugaban ?asa gabanin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.
A wani sa?on bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Bayo Onanuga mataimaki na musamman ga za?a??en shugaban ?asar ya ce Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sun koma gidan da aka tanadar wa shugaban ?asa mai jiran-gado da aka fi sani da ‘Defence House’.
A ranar 24 ga watan Afrilu ne Tinubu ya koma Najeriya bayan hutun kwanaki sama da talatin da ya yi a birnin Paris.
Tinubu dai na fuskantar kalubale daga manyan abokanan takararshi Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na Jam’iyyar Labour wadanda suka shigar da ?ara Kotu suna ?alubalantar nasarar da ya samu a zaben da ya gabata.
Za?en Tinubu da Shettima dai ya zama wani za?e da ya tayar da ?ura a Najeriya ganin yadda Shugaban da mataimakinsa suka fito daga addini guda na Musulunci, lamarin da masu fashin ba?i ke fassara shi a matsayin zabe na rashin adalci.
