Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da rahoton ?ungiyar Tarayyar Turai (EU) game da sakamakon babban za?en 2023 da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban ?asar.
Cikin rahoton nata, ?ungiyar ta ce sunan hukumar za?en Najeriya INEC ta ?aci, musamman saboda gazawa wajen ?ora sakamakon za?en shugaban ?asa a shafin intanet a lokacin da ta yi al?awari tun da farko.
Wata sanarwa daga fadar shugaban ?asa ta bayyana rahoton a matsayin “maras kan-gado da aka ha?a shi ta hanyar dogaro da abubuwan da suka faru a rumfunan za?e ?asa da 1,000 cikin 176,000 da aka ka?a ?uri’a” a ranar za?en na watan Fabrairu.
“Babban za?e na 2023, musamman na shugaban ?asa da Bola Tinubu ya lashe, shi ne mafi inganci da zaman lafiya da aka ta?a yi a Najeriya tun shekarar 1999,” in ji Dele Alake, mai bai wa shugaban ?asa shawara kan ayyuka na musamman.
Kazalika, ya ce babu wata ?wa??warar hujja da EU ko wata ?ungiyar ?asar waje ta gabatar da za ta yi fatali da ingancin za?en na watan Fabrairu, yana mai cewa sauran ?ungiyoyi kamar na rainon Ingila, Commonwealth, da Ecowas, da NBA sun yabi adalci da yadda aka gudanar da shi.
