?ungiyar ?asashen Musulmi ta nemi a ?auki matakin kauce wa sake ?ona ?ur’ani, ‘yan kwanaki bayan wani ya ?ona kwafin littafin mai tsarki a Sweden.
?ungiyar mai mamba 57 ta gana a birnin Jeddah na Saudiyya don lalubo martanin da za su mayar kan ?ona ?ur’anin da Salwan Momika, ?an asalin Ira?i mai shekara 37, ya yi bayan ya tattaka shi a ?ofar wani masallaci a birnin Stockholm.
‘Yan sanda ne suka ba shi kariya kafin ya aiwatar da aniyar tasa, wanda ya ce ya yi hakan ne don ya nuna ‘yancinsa na fa?ar albarkacin baki.
A ranar Lahadi, Organization of Islamic Countries (OIC) ta shawarci ?asashe mambobinta “su ?auki matakin bai-?aya don guje wa afkuwar wula?anta ?ur’ani”, kamar yadda wata sanarwa da suka fitar bayan taron ta bayyana.
“Dole ne mu ci gaba da tunasar da ?asashen duniya game da aiwatar da dokokin ?asa da ?asa da gaggawa, wa?anda suka haramta nuna duk wata ?iyayya ga addinai.”
Lamarin ya jawo zanga-zanga a fa?in duniya, inda ?asashen Musulmi kamar Daular Larabawa da Moroko da Kuwait da Ira?i suka kira jakadan Sweden don nuna ?acin ransu.
