Za?a??en shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta samar da matakai da manufofin da za su sanya al?alai da sauran ma’aikatan Najeriya daina kwa?ayin cin hanci.
Tinubu wanda za a rantsar matsayin shugaban Najeriya nan da kwana 25 masu zuwa ya ce idan aka samar da matakan ?arfafa gwiwa da suka dace, hakan zai tabbatar da kyakkyawan yanayin aiki da manufofi da za su sanya ma’aikata cikin sau?i su iya samu rance don biyan bu?atun rayuwa.
Hakan kuma zai rage kwa?ayin kar?ar cin hanci da rashawa, in ji Tinubu.
Wata sanarwa da wani jami’i a ofishin za?a??en shugaban ?asar, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, ta ambato cewa Tinubu ya yi wannan al?awari ne lokacin da yake ?addamar da rukunin gine-ginen kotun majistare ranar Alhamis a birnin Fatakwal na jihar Ribas.
“Ba za ka yi tsammanin al?alai su yi rayuwa a cikin yanayi maras kyawun gani ba. Wannan na cikin sauye-sauyen da suka wajaba a ?asar nan.
Jazaman ne mu yi ya?i da cin hanci, amma dole ne kuma sai mun yi duba a ?aya ?angaren. “Idan ba a son al?alai su kar?i cin hanci, to kamata ya yi a mayar da hankali wajen kyautata jin da?in rayuwarsu.”
Za?a??en shugaban ya ce rashin tsarin ba da rance ga masu sayen kaya, wanda zai bai wa ma’aikata damar mallakar wata kadara kamar gidaje da motoci shi ne yake ingiza su neman cin hanci da rashawa.
“Idan kana da tsarin ba da rancen sayen kayayyaki, zai iya rage kwa?ayin kar?ar cin hanci. Ba ma son al?alanmu su kaance masu sako-sako da shari’a. Na yi al?awarin za mu yi bitar dukkan irin wa?annan manufofi.”
