Ba Na Goyon Bayan Afuwa Ga ‘Yan Bindiga – Ministan Shari’a

“Babu dalilin yin sulhu ko afuwa ga ‘yan bindiga, babu alfanu a yin haka ba zai haifar da ?a mai ido ba sai ?ara dagula abubuwa, ba na tare da ra’ayin wasu gwamnoni na yin afuwa ga ‘yan bindiga tare da ?aukar ma?udan ku?a?en da ya dace a yi wa talakawa aiki a mi?a musu da sunan rarrashi”.

Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin Ministan Shari’a na ?asa Abubakar Malami SAN yayin amsa tambayar da BBC ta yi masa game da wasu gwamnatocin jihohin da suke yi wa masu satar mutane domin neman kudin fansa da ‘yan fashin daji afuwa har ma da yi musu hasafi, inda ya bayyana cewa ba shi da wannan ra’ayin.

”Hakan bai dace ba, duk wanda ya yi ganganci to shi ma a yi masa gangancin, a matsayina na babban lauya gwamnatin Najeriya, bani da tunani na yafiya ga wanda ya mayar da kashe mutum al’ada, ya dauki rayuwar al’umma a bisa gilla,” in ji ministan.

Ya kuma kara da cewa: “Yan Najeriya miliya dari biyu suna hakkin su zauna lafiya cikin kwanciyar hankali da lumana, don haka idan mutum daya, ko biyu,ko ashirin ko hamsin suka zabi daukar rayukan ‘yan Najeriya kan tsari na gilla, hakki na ne na ministan shari’a na kasa in mayar musu martani a kan tsari na daukar rayukansu”.

Game da batun da ake yi cewa kamar laifukan da wadannan mutane ke aikatawa gwamnatin tarayya ita ke da hurumi a kai, sannan kuma kamar ba ta dauki wani mataki ba na shari’a, sannna su jihohin suke yafe musu kamar ita gwamnatin Najeriya ta zuba musu ido ba su dauki wasu matakai a kan masu yafewa ‘yan bindigar ba.

Amma kuma minsitan ya sake bayyana cewa “Shi yasa na ce a ko wace jiha akwai manyan lauyoyin gwamnati da ya kamata su shigo ciki tare da hukmomin ‘yansanda na ko wace jiha, tun da an bawa kowanne dama.”

Related posts

Leave a Comment