Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar kamfanonin jiragen saman da aka za?a domin jigilar mahajjatan bana sun ?i yarda su sa hannu a kan yarjejeniya da Hukumar Aikin Hajji ta ?asar saboda rikicin Sudan.
An ruwaito cewa Wakilan kamfanonin jiragen sun ha?a da na Air peace da Azman Air da Max Air da kuma Aero Contractors.
Tun farko an shirya kamfanonin za su rattaba hannu ne ranar Alhamis, amma yanzu an ?age sai Talata mai zuwa, saboda wakilan kamfanonin sun nemi a ba su damar tattaunawa da shugabanninsu.
Sai dai jirgi ?aya da zai yi aikin na ?asar waje shi ne Fly Nas kuma tuni ya rattaba hannu, inda a yarjejeniyar aka amince zai yi jigilar maniyyata 28,000 kimanin kashi 40% na mahajjatan bana daga Najeriya.
Rufe sararin samaniyar Sudan saboda rikici, zai shafi jigilar aikin hajjin bana daga wasu ?asashen Afirka, saboda ita ce hanya mafi gajarta zuwa Saudiyya.
Idan aka sake sabuwar yarjejeniya tsakanin Hukumar NAHCON da masu kamfanonin jiragen sama, akwai yiwuwar ku?a?en aikin hajjin za su ?aru, a kuma sake nazari kan tsare-tsaren aikin Hajjin.
A watan Afrilu ne NAHCON ta ?ayyade mafi ?arancin ku?in da za a biya na aikin hajji daga naira miliyan 2.88 zuwa naira miliyan 2.9.
