Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya amince da kashe dala miliyan takwas da rabi – fiye da naira biliyan uku – wajen aikin kwashe ‘yan ?asar daga ?asashe hu?u ma?otan Ukraine sakamakon ya?in da ake yi a can.
Ma’aikatar harkokin waje da ha?in gwiwar ta agaji ne za su gudanar da aikin kwashe ‘yan ?asar kusan 5,000 daga ?asashen Poland da Ramania da Slovakia da Hungary.
?aramin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada ya fa?a wa manema labarai a yau Laraba jim ka?an bayan kammala taron Majalisar Zartarwa cewa za a tura jirage uku don gudanar da aikin.
Jiragen sun ?unshi na kamfanin Air Peace biyu da kuma na Max Air ?aya.
Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen ta ce za a fara gudanar da aikin ?ebo su bayan sun tsallaka ma?wabta daga Ukraine sakamakon fafatawar da ake yi tsakanin dakarun Rasha da na ?asar.
