2023: Kalaman Obasanjo Da Ango Abdullahi Goyon Baya Ne Ga Hamza Al-Mustapha – Wali

An bayyana kalaman da tsohon shugaban kasa Obasanjo da shugaban Dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi suka yi na sukar ‘yan takarar manyan Jam’iyyu Tinubu da Atiku da cewar alama ce ta gamsuwar su da takarar Hamza Al-Mustapha.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar Matasan Najeriya Alhaji Abdullahi Abubakar Wali a yayin zantawa da manema labarai a Abuja.

Abubakar Wali ya kara da cewar ga dukkanin wanda ya saurari bayanan wadannan Dattawa biyu Obasanjo da Ango Abdullahi zai fahimci cewar sun fito fili sun sauke nauyin da ke a kansu matsayin su na Dattawa, inda suka ankarar da jama’a raunin da ‘yan takarar shugabancin ?asa na APC da PDP suke dashi bisa ga jagoranci, sakamakon tsufa da kuma rashin lafiya.

“Idan jama’a za su tuna Obasanjo ya shaida mutumin da ya dace Najeriya ta samu a yanzu wanda zai kai ?asar ga gaci, kuma dukkanin sharuddan da ya gindaya ?an takarar Shugaban ?asa na Jam’iyyar AA Hamza Al-Mustapha ya cika su”.

Abubakar Wali ya kara da cewar a matsayin ?ungiyar su ta Matasan Najeriya sun ha?u gaba ?aya bangaren Kudu da Arewa sun za?i Hamza Al-Mustapha matsayin mutum guda daya tilo da ya dace da zama shugaban ?asa saboda gogewa da kwarewar shi a mulki.

Daga karshe ya yi kira ga ‘yan Najeriya gaba daya da su yi watsi da wadancan baragurbi da manyan Jam’iyyu suka tsayar, su goyi bayan Hamza Al-Mustapha domin dawo da Najeriya hayyacinta.

Related posts

Leave a Comment