Sabon babban sufeton ‘yan sandan Najeriya na ri?o, Olukayode Adeolu Egbetokun ya ?addamar da abin da ya kira tsare-tsaren aiki don farfa?o da yardar jama’a a kan ‘yan sanda.
Babban sufeton ya ?addamar da sabbin manufofin ne yayin wani taron ?addamar da salon shugabancinsa a shalkwatar ‘yan sanda ta ?asa da ke Abuja.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce a cikin manufofin babban sufeton akwai kafa jami’an kai ?auki cikin hanzari mai taken Quick Intervention Squad wanda zai ha?ar da ‘yan sandan kwantar da tarzoma da za su kasance shiri don kashe wutar fitintinu da aikata laifuka.
Ya kuma ce shugabancinsa zai tabbatar da aiki da fasahohin zamani kamar ?ididdigar al?aluma da harkokin tattara bayanan sirri don bun?asa ?wazon ‘yan sanda.
Haka kuma, babban sufeton zai tabbatar da aiki da wani tsarin martabawa da ba da lada don ?ara ?wazo da ?arfafa gwiwar jajirtattun jai’an rundunar. Yayin taron na ranar Juma’a manyan jami’an ‘yan sandan Najeriya daga fa?in ?asar ne suka halarta.
