Kungiyar tabbatar da adalar shugabanci a Najeriya (TLA) ta yi kira da babbar murya ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi ko in kula da kiraye-kirayen wa?anda ta bayyana su wa?anda aka dauki hayarsu domin bata suna da dakushe ayyukan alheri da shugaban kamfanin NNPC na ?asa Malam Mele Kyari ke yi.
A takardar sanarwa da kungiyar ta fitar wanda aka rarraba wa manema labarai a birnin tarayya Abuja, Shugaban kungiyar Dr. Musa Adam ya bayyana cewar an yi wani gangami na daukar nauyin ya?a labaran ?anzon kurege akan Mele Kyari tun bayan ?i?i ?a?ar da ta faru na sallamar tsohon gwamnan babban bankin ?asa Emefiele.
Adam ya bayyana cewar guguwar ya?i da kamfanin NNPC da Mele Kyari a kafafen watsa labarai ta faro ne tun bayan gano man fetur a jihohn Gombe da Bauchi wanda shugaban ?asa ya kaddamar a shekarar a watan Nuwambar 2022 da kuma aikin hako mai da ya faru kwanan nan a yankin Obi/Keana na Jihar Nasarawa a 21 ga Watan Maris na 2023.
Sanarwar ta bayyana cewar irin wannan namijin kokari da Malam Mele Kyari ya yi a Shugabancin NNPC wani abu ne wanda har abada ba za a manta dashi na ciyar da ?asa gaba.
Sun kuma bayyana cewar “Kyari ya samar da taswirar hanyoyi domin dacewa da tafiyar zamani wanda ya taimaka wajen samun nasarar shugabancin nasa wanda ya zama abin misali da kwatance. A kowane wata kamfanin NNPC ya wallafa dukkanin abin da ya shigo ko ya fita a kamfanin a kafafen sadarwar zamani wanda hakan bai taba faruwa ba a tarihin tattalin arzikin Najeriya”.
Kungiyar ta bayyana Shugaban kamfanin na NNPC a matsayin mutum mai kamala da tsari kuma a gefe mutum ne Musulmi mai tsoron Allah wanda ya ke sadaukar da dukiyar sa wajen taimakon jama’a da basu dashi a cikin ?asa.
Sun kuma bu?aci Shugaban ?asa Tinubu da ya yi watsi da dukkanin makiya da Mahassadda wa?anda ke dakon labaran karya a gidajen jaridu da zimmar haifar da gaba tsakanin shugaban kasa da Shugaban NNPC a daidai gabar da Najeriya ke kokarin fita daga matsin tattalin arziki.
