Za Mu Bar Najeriya Idan Peter Obi Ya Fadi Zabe – Babachir Lawal

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Babachir Lawal, ya ce shi da wasu jiga-jigan siyasa masu goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, za su koma Kamaru idan dan takarar ya fadi zaben shugaban kasa a 2023.

Tsohon SGF ?in ya bayyana haka ne a jiya Litinin yayin wata tattauna wa da Obi da masu ruwa da tsaki na LP daga Arewa maso Gabas a Abuja.

Lawal, jigo a jam’iyyar APC mai mulki, ya kuma bayyana mamakinsa da cewa APC ba ta kore shi daga jam’iyyar ba, duk da adawar sa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu.

Ya kara da cewa zaben shugaban kasa na 2023 ya zama dole Obi ya lashe, idan aka yi la’akari da halin da kasar nan ke ciki.

“Ina cikin APC kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar, amma ina tafiyar Peter Obi/Yusuf Datti. Har yanzu APC ba ta kore ni ba. “Ban san abin da suke jira ba.

“Muna son (Obi) ya ci zaben nan kuma dole ne ya ci wannan zaben. Idan muka fadi wannan zabe, dukkanmu za mu yi hijira zuwa Kamaru saboda kunya da wulakanci na rashin cin nasara.

Related posts

Leave a Comment