Sakon Tallafin Tinubu Na Raba Kudi Ga ‘Yan Najeriya Ba Gaskiya Ba Ne – Kwamitin Neman Zabe


Wata sanarwa da tawagar ya?in neman za?en Tinubu ta fitar ta ce sa?on da ake ya?awa na ?arya ne kuma ba daga wurinsu ya fito ba.

“Muna tabbatar da wannan sa?on na ?arya ne saboda ba daga wajenmu ya fito ba,” a cewar Festus Keyamo kakakin tawagar kamfe ?in Tinubu/Shettima kuma ?aramin Ministan ?wadago na Najeriya.

Mista Keyamo ya zargi jam’iyyun adawa da “yun?urin tura sa?onni marasa kan-gado da zimmar samun ?uri’un ‘yan Najeriya”.

A ranar Laraba Bola Tinubu ya fa?a wa BBC cikin wata hira cewa tabbas shi mai ku?i ne, duk da cewa wasu na yi masa hassada.

“Ba na gudun a ce ni mai ku?i ne, amma dai wasu na yi min hassada game da dukiyata,” in ji shi.

Tinubu mai shekara 70 ya kuma bayyana cewa tun da ya sauka daga gwamnan Legas a shekarar 2007 bai sake ri?e mu?ami ba ko kuma kwangilar gwamnati.

Kamar yadda ta yi a za?ukan 2015 da 2019, wannan karon ma jam’iyyar APC mai mulki na neman tallafin ku?in ya?in neman za?e daga ‘yan Najeriya.

Magoya bayan jam’iyyar sun wallafa sa?onnin neman taimakon sau da dama a shafukansu na sada zumunta, cikinsu har da Bashir Ahmad – mataimaki na musamman ga Shugaba Buhari kan kafofin sada zumunta.

Kamfe ?in Tinubu/Shettima ta ?ir?iri shafin neman taimakon ne a dandalin blessmi, inda ake neman mutane su tura ku?i ta wani asusun banki.

“Ku tallafa wa kamfe ?inmu don taimakawa wajen cimma muradanmu kan ?asarmu mai daraja,” a cewar sa?on da ke kan shafin.

Zuwa yanzu babu bayanan adadin ku?in da suka tara na tallafin amma za a ci gaba da kar?a har nan da kwana 76.

Related posts

Leave a Comment